Manyan hafsoshin tsaron kasar da sufeto janar na yan sanda da kuma manyan jami'an tsaro duk suma suna cikin tattaunawar.
An gayyaci sarkin Musulmi da Shugaban kungiyar Kiristocin-CAN duk don su bada tasu gudumuwar a taron.
Wannan tattaunawar na zuwa ne a daidai lokacin da Kasar ke fuskantar matsalolin tsaro mussamman ayyukan yan'BOKO Haram.